DR HAFIZ IBRAHIM AHMED PHD YA TALLAFAWA MUTANE A KARAMAR HUKUMAR KUSADA DOMIN JINKAI.

EMPOWERMENT EMPOWERMENT

Posted by dpek on 2026-03-24 08:33:09 |

Share: Facebook | Twitter | Whatsapp | Linkedin Visits: 18


DR HAFIZ IBRAHIM AHMED PHD YA TALLAFAWA MUTANE A KARAMAR HUKUMAR KUSADA DOMIN JINKAI.

A wani mataki na nuna tausayi da kulawa ga al’umma, Mai Bai wa Gwamnan Jihar Katsina Shawara kan harkokin wutar lantarki da makamashi (SA Power and Energy), Hafiz Ibrahim Ahmad PhD, ya tallafa wa al’ummar ƙaramar hukumar Kusada da buhunan shinkafa sama da 300 tare da kuɗaɗe domin rage musu radadin rayuwa da kuma ƙarfafa zumunci a tsakanin al’umma.An gudanar da rabon tallafin ne a Sabon Garin Dangamau da ke cikin ƙaramar hukumar Kusada, inda Mataimakin Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Makamashi, Engr. Abdulaziz Abdullahi Kabir, tare da Shugaban Ƙaramar Hukumar Kusada, Hon. Sani Aminu, suka jagoranci rabon kayan ga al’umma tare da tabbatar da cewa tallafin ya kai ga waɗanda suka fi buƙata.Tallafin ya jawo farin ciki da godiya daga al’ummar yankin, inda suka bayyana cewa irin wannan taimako na ƙara ƙarfafa musu gwiwa tare da nuna cewa shugabanni na tuna da su a kowane lokaci. Haka kuma sun yaba da irin ƙoƙarin da Hafiz Ibrahim Ahmad ke yi wajen taimaka wa al’umma tare da tallafa musu a fannoni daban-daban na rayuwa

Additional Image
Leave a Comment: